Monday, September 25, 2023

TAƘAITACCEN TARIHIN KURYA MADARO

Fadar Uban ƙasar Kurya Madaro
  • Kurya Madaro gunduma ce, a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kaura Namoda dake Jahar Zamfara, arewa maso yammacin Nigeria.
  • Kurya Madaro an kafa ta bisa turbar musulunci a karkashin jagorancin  Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo fiye da shekara ɗari biyu da suka wuce.
  • An sami sunan wannan gari daga yawaitar itatuwan Kurya shi yasa ake kiranta da suna Kurya ita kuma sarautar Madaro, an same tane sanadiyyar wata rijiya da aka isko mai ruwa kamar Madara,  Adamu Kada da Ja'oji su suka kafa wannan gari na Kurya Madaro inda Babban su Dan Abore ya hurce garin Rawayya inda ya kafa nasa gari mai suna Rawayya, dukkansu ƙabilar Jallawane.

    KURYA MADARO TA SAMU  JAGORANCIN SARAKUNA GUDA GOMA SHA HUDU (14) A HALIN YANZU WUDANDA NA HADA DA:

  1. Madaro Adamu Kada
  2. Madaro Ja'oji
  3. Madaro Usman Mani
  4. Madaro Aliyu Dan Kada
  5. Madaro doshiro
  6. Madaro Atto
  7. Madaro  Ciwake
  8. Madaro Muhammad Na Gabake
  9. Madaro Adamu
  10. Madaro  Muhammadu Ɗan Alo
  11. Madaro Amadu Dan Iro
  12. Madaro Sama'ila
  13. Madaro muhammadu salati
  14. Madaro Mahmud Muhammadu Salati shine Ubanƙasar Kurya Madaro.                   Madaron KuryaMalam Abdulkadir (Liman Masallacin Jumuah na II, Kurya Madaro)

TAƘAITACCEN TARIHIN KURYA MADARO

Fadar Uban ƙasar Kurya Madaro Kurya Madaro gunduma ce, a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kaura Namoda dake Jahar Zamfara, arewa maso yammacin Nige...